Tambaya Da Amsa

Tambaya da Amsa: Taƙaitaccen tarihin Marigayi Sheikh Ɗahiru Bauchi

Informações:

Sinopsis

Shirin Tambaya da Amsa tare da Nasiru Sani, bisa al'ada kan amsa tambayoyin da masu sauraro suka aiko, inda a yau guda cikin tambayoyin da wannan shiri ya amsa shi ne buƙatar taƙaitacce tarihin fitaccen Malamin Islaman nan a Najeriya kuma jigo a Dariƙar Tijjaniya, shehu Usman Dahiru Bauchi wanda Allah ya yiwa rauswa a ranar 27 ga watan Nuwamban shekarar da muke ta 2025 . Don samun amsar wannan tambaya ce wakilin RFI a jihar Bauchin Najeriya Ibrahim Malam Goje ya zanta da Dr Fathi Sheikh Dahiru Usman Bauchi, daya daga cikin 'ya'yan marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi, kuma daya daga cikin wadanda suka taɓa rubuta littafi a kan marigayin. Ku latsa alamar ƙari don jin amsar wannan tambaya da sauran tambayoyin da ke ƙunshe cikin wannan shiri tare da Nasiru Sani.