Wasanni

Shirye-shiryen sun yi nisa na fara gasar Firimiyar Najeriya ta baɗi

Informações:

Sinopsis

Shirin Duniyar Wasanni a wanan mako ya yi dubu ne kan shirye-shiryen fara gasar Firimiyar Najeriya ta kaka mai zuwa, kuma tuni hukumar shirya gasar Firimiyar Najeriya wato NPFL, ta sanya 22 ga watan Agusta mai zuwa a matsayin ranar soma kaka ta baɗi. An dai ji shugaban hukumar shirya babbar gasar ta Najeriya Gbenga Elegbeleye na cewar, suna duba yuwuwar soma amfani da na’urar VAR a gasar mai zuwa, baya ga kuma inganta kayayyakin gudanarwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh............