Wasanni

Kwara da Rivers sun lashe kofin ƙalubale na Najeriya a bangaren Mata da Maza

Informações:

Sinopsis

Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan makon tare da Micheal Kuduson ya mayar da hankali ne kan wasannin ƙarshe na gasar cin kofin ƙalubale na Najeriya, wadda yanzu ake kira President Federation Cup, da aka gudanar a filin wasa na Mobolaji Johnson Arena da ke birnin Lagos.  Da wasan mata aka fara, inda aka ɓarje gumi tsakanin ƙungiyar kwallon ƙafa ta Nasarawa Amazons da ke garin Lafia da Rivers Angels ta birnin Fatakwal a wansan ƙarshe karo na 10 a wannan gasa, ɓangaren mata. Ƴan matan Nasarawa ne suka fara saka ƙwallaye biyu a ragar Rivers, ƙwallayen da Rukayyat Shola Sobowole ta ci, a yayin da Taiwo Ajibade da Taiwo Afolabi suka farke wa Rivers. Haka dai aka tashi wannan wasa biyu da biyu, Rivers mairiƙe da kofin ta sake daukawa a wannan karon a bugun daga kai sai mai tsaron raga da ci 4 da 2. Bayan wasan na mata, da baye-bayen kyautuka ne aka shiga wasan maza, inda kungiyar ƙwallon ƙafa ta Kwara United ta garin Ilorin ta doke Abakaliki FC da ci 4 da 3 a bugun daga kai sai mai tsaron raga, bayan da aka buga can