Wasanni

Yadda wasanni suka gudana bayan fara sabuwar kakar ƙwallon ƙafa a Turai

Informações:

Sinopsis

Shirin 'Duniyar Wasanni' a wannan makon ya mayar da hankali ne a kan yadda aka fara sabuwar kakar ƙwallon ƙafa a bana a manyan Lig-Lig na sassan nahiyar Turai. Manyan wasannin dai sun haɗa da na Firimiyar Ingila, La Ligar Spain, da kuma gasar Ligue 1  na ƙasar Faransa. Kamar yadda za a ji cikin shirin tare da Khamis Saleh, Liverpool ce ta fara buɗe sabuwar kakar wasa a Firimiyar Ingila inda ta lallasa Bournemouth da ƙwallaye 4-2.