Wasanni

Yadda Ashraf Hakimi ya lashe gwarzon shekara na Afrika karon farko

Informações:

Sinopsis

Shirin "Duniyar Wasanni" tare da Khamis Saleh a wannan lokaci zayyi duba ne kan ƙyautar gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafan Afirka da Achraf Hakimi na Morocco ya lashe. A makon daya gabata ne Hukumar Kwallon Ƙafar Afrika CAF, ta bayar da kyautuka ga zaratan ƴan wasan nahiyar da suka nuna bajinta a wannan shekarar da muke bankwana da ita. A yayin bikin da ya gudana a birnin Rabat na ƙasar Morocco, hukumar ta CAF ta sanar da ɗan wasan baya na tawagar ƙasar ta Morocco wanda kuma ya ke yi wa ƙungiyar PSG wasa Achraf Hakimi,  a matsayin wanda ya lashe ƙyautar gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Afirka a wannan shekarar. Hakimi ya samu nasarar ce bayan doke shahararrun ƴan wasan nahiyar da suka taɓa lashe kyautar irinsu Mohamed Salah na Masar da ke taka leda a Liverpool,  da kuma Victor Osimhen na Nigeria da ke wasa a Galatasaray. Wannan ne dai karo na farko da ɗan wasan ya taɓa lashe ƙyautar, bayan da a karo biyu a jere ya na ƙarewa a mataki na biyu, a shekarar 2023 da Victor Osimhen ya lashe da kuma 2024 da Ademola Loo