Kasuwanci
Yadda kasuwancin Internet ke bunkasa tattalin arzikin kasashe masu tasowa
- Autor: Vários
- Narrador: Vários
- Editor: Podcast
- Duración: 0:10:07
- Mas informaciones
Informações:
Sinopsis
A wannan mako shirin ya tattauna ne kan rawar da kasuwancin Intanet ke takawa wajen bunkasar tattalin arzikin kasashe irinsu Najeriya. Kasuwanci ta internet da ake kira da e-commerce a turance, na taka muhimmiyar rawa wajen sauya yadda ake gudanar da harkokin siye da siyarwa a duniya tare da habakar tattalin arziki.A Najeriya, masana sun yi ittifakin cewa kasuwanci internet wato e-commerce na kawo sauyi ga tattalin arzikin kasar, tare da samar da ci gaba ta fuskoki da dama, da kuma samar da ayyukan yi a tsakanin al’ummar kasar.Duk da cewa an hakkikance kasuwanci ta internet na bunkasa tattalin arziki a Najeriya, akwai tulin kalubale da ya kamata a magance, masamman karancin wayewa game da harkokin kasuwanci ta Internet ga jama'a, da wargajewar kasuwa.Masana sun yi nuni da cewa, kasuwanci ta internet na bayar da damar da za ta iya haifar da ci gaban tattalin arziki a Najeriya, amma hakan na bukatar tallafi da aiwatar da wasu manufofi, wandanda za su samar da kyakkyawan yanayi ta fuskar kasuwanci da tattalin ar