Kasuwanci

Gobarar kasuwar kayan gwanjo mafi girma a duniya ya tagayyara ƴan kasuwa a Ghana

Informações:

Sinopsis

Shirin 'Kasuwa a kai Miki Dole' na wannan makon ya mayar da hankali kan asarar da ƴan kasuwar Kantamanto na ƙasar Ghana suka tafka sakamakon gobarar da ta lakume kasuwar ƙurmus.Hukumomi a Ghana sun ce mummunar gobara da ta tashi a kasuwar kayan gwanjo mafi girma a duniya ranar 2 ga watan Janairun wannan shekara ta 2025 ta lakume sama da shaguna dubu 7 tare da tagayyara ƴan kasuwa sama da dubu 30, inda akalla mutun guda ya mutu wasu 14 suka jikkata.