Lafiya Jari Ce

Matsalar mace-macen mata a lokacin haihuwa ta ta'azzara a jihar Kaduna

Informações:

Sinopsis

Shirin Lafiya Jari Ce tare da Azima Bashir Aminu  ya mayar da hankali yadda wasu alƙaluman baya-bayan nan a jihar Kaduna ta Najeriya ke nuna yadda ake samun ƙaruwar matan da ke mutuwa yayin goyon ciki ko haihuwa, wanda ke da nasaba da yadda jama’a ke ƙauracewa asibitoci walau a lokacin awo ko kuma haihuwa, wannan shi ne maudu’inmu na wannan mako sai ku biyomu. Wani binciken baya-bayan nan ya gano cewa matsalar ta mace-macen mata masu juna biyun tafi ta’azzara a ƙananan hukumomin jihar ta Kaduna guda 7 ciki har da Zaria. ‎Ɗimbin mata ne ke kafa hujja da halin rayuwa a matsayin dalilin da ke nesantasu da asibiti a lokacin goyon ciki ko haihuwa, kodayake masana na ganin babu wani dalili na ƙin kai mai juna asibiti, tare da zuba mata ido musamman idan haihuwa ta zo da tirjiya, sai dai wasu bayanai na cewa gwamnatoci a matakai daban-daban na sauƙaƙa tsarin karɓar haihuwar musamman ga marasa ƙarfi. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.