Al'adun Gargajiya

Bikin Kalankuwar farfaɗo da al'adun Hausawa a jihar Kano ta Najeriya

Informações:

Sinopsis

Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali ne kan Kalankuwar farfaɗo da al'adunmu Hausawa a jihar Kano ta arewacin Najeriya, a wani yanayi da al'umma ke fuskantar matsalar gushewar tarin al'adu a mataki daban-daban. Yayin wannan bikin Kalankuwa dai an duba fannoni daban-daban na al'adu kama daga Kiɗan gargajiya da Waƙa baya ɓangarorin wasanni da dama, bikin da ya samu halartar sarakuna da dama. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...