Bakonmu A Yau
Dr Yahuza Getso kan gudunmawar ƴan sa kai a yaki da ta'addanci a Najeriya
- Autor: Vários
- Narrador: Vários
- Editor: Podcast
- Duración: 0:03:28
- Mas informaciones
Informações:
Sinopsis
A Najeriya jami’an tsaro na ‘Yan Sa-kai ko Vigilante ko kuma na ‘Civilian JTF’ da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya na taka rawa wajen taimakawa jami’an tsaro na gwamnati wajen yaƙi da ta’addanci da sauran miyagun laifuka. Sai dai duk da ƙokarin jami’an tsaron na Sa-Kai ra’ayoyi sun banbanta, dangane da rawar da suke takawa, inda wasu ke yaba musu ɗari bisa ɗari, yayin da wasu ke neman a yi gyara kan tsarin ayyukansu la’akari da kura-kuran sukan tafka ta hanyar wuce gona da iri a wasu lokuta da dama.Kan haka Nura Ado Suleiman ya tattauna da masanin tsaro a tarayyar Najeriya, Dakta Yahuza Getso.