Bakonmu A Yau

  • Autor: Vários
  • Narrador: Vários
  • Editor: Podcast
  • Duración: 1:21:16
  • Mas informaciones

Informações:

Sinopsis

A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.

Episodios

  • Najeriya na shirin shigar da shanu daga Denmark

    04/06/2025 Duración: 03min

    Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da shirinta na shigar da wasu shanu daga ƙasar Denmark, a ƙoƙarinta na rage kashe kuɗaɗen shigar da madara da kuma wadatarta a ƙasar, wanda yawansu ya kai dala biliyan 1.5 duk shekara. Duk da ikirarin kasancewarta ƙasar da ta fi kowacce yawan shanu a nahiyar Africa, amma Najeriya na samar da tan dubu 700 na madara duk shekara ne, ƙasa da tan miliyan 1.6 da ƴan ƙasar ke buƙata. To sai dai a zantawarsa da RFI Hausa, sakataren Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah ta Najeriya Baba Usman Ngerzelma ya ce babu buƙatar ɗaukar wannan mataki da za’a mayar da hankali kan shanun da ake da su a ƙasar.Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu da Rukayya Abba Kabara..........

  • Ƙungiyar Amnesty ta zargi sojojin Najeriya da kashe ƴan-sa-kai a Zamfara

    03/06/2025 Duración: 04min

    Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International a Najeriya ta yi zargin cewa jirgin sojin saman ƙasar ya yi ruwan bamai-bamai kan jami’an sakai tare da kashe akalla 20 da jikkata wasu da dama a ƙauyukan Maraya da Wabi da ke ƙaramar hukumar Maru na jihar Zamfara. Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar jiya Litinin, ta ce lamarin kai tsaye ya shafi jami’an sakai da suka taru domin tunkarar ƴan bindiga da suka kai hare-hare a ƙauyukan nasu ranar Asabar.  A tattaunawarsa da Ahmad Abba, Daraktan Amnesty International a Najeriya, Malam Isa Sunusi, ya fara da bayani kan yadda lamarin ya auku.

  • Har yanzu akwai sauran gawarwakin da ba a gano ba - Dauda Mokwa

    02/06/2025 Duración: 03min

    Kwanaki biyar bayan da ambaliyar ruwa ta afka wa garin Mokwa na jihar Neja a tarayyar Najeriya, mahukunta a yankin sun ce adadin mutanen da aka tabbatar da cewa sun rasa rayukansu sun kai ɗari biyu. A cewa Sakataren ƙaramar hukumar ta Mokwa Dauda Liman Mokwa, yanzu ana kyautata zaton cewa akwai gawarwaki da dama da ba a kai ga gano su ba, ko dai a cikin ruwa ko kuma a ƙarƙashin gine-ginen da suka rufta. Ku latsa alamar sauti don jin tattaunawarsa da Abdulkarim Ibrahim Shikal..............

  • Kwamrade Ishaq Ja’afar kan cikar gwamnatin Tinubu shekaru biyu kan karaga

    29/05/2025 Duración: 03min

    Yau Alhamis shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ke cika shekaru 2 a kan karagar mulki, bayan rantsuwar kama aikin da ya yi a rana mai kamar ta yau, cikin shekarar 2023. La’akari da yadda ra’ayoyi suka banbanta a tsakanin ƴan ƙasar a kan manufofi da sauran matakan wannan gwamnati.......ya sa muka nemi tsokacin Kwamrade Ishaq Ja’afar Ɗalhat Gandun Albasa, mai sharhi kan lamurran yau da kullum a Najeriyar. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu da Nura Ado Suleiman...........

  • Dr Abdullahi Shehu kan rawar da ECOWAS ta taka wajen yaƙi da rashawa

    28/05/2025 Duración: 03min

    Yayin ake ci gaba da bikin cika shekaru 50 da kafa Ƙungiyar Haɓaka Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika ECOWAS/CEDEAO, a wannan karo za mu yi dubi a game da wasu daga cikin muhimman ayyukan da ƙungiyar ta yi a fagen yaƙi da rashawa. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna Dr Abdullahi Shehu, tsohon jakadan Najeriya a Rasha, kuma wanda ya jagora hukumar ta GIABA tsawon shekaru 8.  Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar tasu...........

  • Air Comodore Tijjani Baba Gamawa kan bikin cikar ECOWAS shekaru 50 da kafuwa

    27/05/2025 Duración: 03min

    Ranar 28 ga watan Mayu, wato gobe Laraba kenan, Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afrika ECOWAS, ke cika shekaru 50 da kafuwa.An dai samar da ƙungiyar ne cikin watan Mayun shekarar 1975 a birnin Legas, inda a wacccan lokacin ta ƙunshi ƙasashe 15. A tsawon lokacin da ta shafe bayan kafuwarta, ECOWAS ta taka rawa muhimmiyar rawa ta fuskar tsaro, ciki kuwa har da kawo ƙarshen yaƙe-yaƙen da suka nemi wargaza ƙasashen Saliyo da Liberia. Kan haka ne kuma Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da, Air Comodore Tijjani Baba Gamawa ɗaya daga cikin sojojin da suka bayar da gudunmawa a waccan lokaci.

  • Alhaji Nouhou Magaji kan ƙorar ma'aikatan ƙetare a ɓangaren man fetur da Nijar ta yi

    26/05/2025 Duración: 03min

    Gwamnmatin Jamhuriyar Nijar ta buƙaci ƴan asalin ƙasashen ƙetare da ke aiki a ɓangaren man fetur da su fice daga ƙasar kafin ranar 31 ga wannan wata na Mayu. Mafi yawan waɗanda matakin zai shafa ƴan ƙasar China ne da ke aikin haƙowa, da tacewa, sai kuma waɗanda ke fitar da mai ta bututu zuwa ƙetare.  Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar Alhaji Nouhou Abdou Magaji da Abdoulkarim Ibrahim Shikal.....

  • Janar Alwali Kazir kan matakin ECOWAS na samar da rundunar yaki da ta'addanci

    23/05/2025 Duración: 03min

    Kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ta ECOWAS ta bayyana shirin kafa sabuwar rundunar hadin kai wadda za ta dinga yaki da yan ta'addan da suka addabi yankin. Wannan na da cikin shirin shugabannin yankin na dakile ayyukan ta'addanci, da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Janar Kape Alwali Kazir mai ritaya a dangane da wannan shiri.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

  • Senator Ikra Bilbis kan cika shekaru 18 da fara watsa shirye-shiryen RFI Hausa

    22/05/2025 Duración: 03min

    An gudanar da ƙwarya-ƙwaryar biki don murnar cika shekaru 18 da buɗe Sashen Hausa na Radio France International, inda aka samu halartar manyan baƙi da suka haɗa da sarakunan gargaji, ƴan siyasa da kuma masu sauraren rediyon da sauran kafafensa na yaɗa shirye-shirye. Ɗaya daga cikin manyan baƙi a taron shi ne Distinguished Senator Aliyu Ikra Bilbis wanda ya bayyana mahangarsa a game da waɗannan shekaru 18 na RFI Hausa. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu da Abdoulkarim Ibrahim Shikal..............

  • Malam Bashir Ibrahim Idris kan cika shekaru 18 da kafuwar RFI Hausa

    21/05/2025 Duración: 03min

    A yau 21 ga watan Mayun 2025, shekaru 18 kenan da Radio France International ya fara yaɗa shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa, wanda kuma shi ne harshen na farko daga Afirka da RFI ta fara yaɗa shirye-shiryenta da shi. Malam Bashir Ibrahim Idris, shi ne Babban Editan RFI Hausa, ya yi muna ƙarin bayani a game da yadda rediyon ya fara da kuma irin ci gaba da ya samu a waɗannan shekaru. Ku latsa alamar sauti don jin tattaunawar da Ƙaribullah Abdulmajid Namadobi ya yi da shi...........

  • Gamatie Mahamadou Yansanbou-Kan ta'addancin masu ikirarin jihadi kan ayarin motocin dakon kaya

    20/05/2025 Duración: 03min

    Aƙalla Direbobin manyan motoci uku sun mutu  yayin da wasu da dama suka jikkata a wani saban  harin da ƴanta’adda masu ikrarin jihadi suka kai kan ayarin motocinsu akan hanyar Burkina Faso zuwa Jamhuriyar a rana lahadin da ta gabata. Wanan ne karo na biyu cikin kasa da shekaru guda da ƴan bindigar ke farwa wadanan motoci tare da banka musu wuta.A kan wanan abokin aiki Oumar  Sani ya tattauna da Gamatie Mahamadou Yansanbou, magatakarda kungiyar direbobin manyan motoci UTTAN a Jamhuriya Nijar ga kuma yadda zantawarsu ta gudana.Danna alamar saurare domin jin cikakkiyar tattaunawar.

  • Abdullahi Jalo akan ƙorafin arewa a game da jarabawar JAMB

    19/05/2025 Duración: 03min

    Da aalam dai har yanzu da sauran rina a kaba ga hukkumar JAMB, mai shirya jarabawar shiga manyan makarantu a Najeriya a game da matsalar da aka samu a lokacin jarabawar wannan shekarar sakamakon ƙorafin da wasu jihohin arewacin ƙasar ke yi akan ware wasu jihohi huɗu na kudu da hukumar ta yi don sake zana jarawabar. Tuni dai wasu suka yi barazanar zuwa kotu tare da kira ga gwamnati da ta saka baki a lamarin. Kan haka ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Barrister Abdullahi Jalo, masanin doka.

  • Farfesa Sheriff Almuhajir kan makomar yankin Tafkin Chadi a ɓangaren tsaro

    16/05/2025 Duración: 03min

    Babban Hafsan tsaron Najeriya, Laftanar Janar Christopher Musa ya ce baya ga amfani da makamai wajen tinkarar mayakan Boko Haram, farfado da Tafkin Chadi zai taimaka wajen samarwa jama'ar yankin sana'oi. Wannan ya biyo bayan ziyarar aikin da ya kai Maiduguri bayan kazaman hare haren da boko haram ta kai cibiyoyin soji.Dangane da wannan bukatar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da wani mutumin yankin, Farfesa Sheriff Muhammad Almuhajir.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

  • Umar Saleh Gwani kan faɗuwar jarabawar JAMB a Najeriya

    15/05/2025 Duración: 03min

    Hukumar kula da jarabawar shiga manyan makarantu a Najeriya ta JAMB ta nemi gafarar jama'ar kasar saboda matsalolin da aka samu wajen jarabaswar bana, wadda ta kai ga dalibai sama da miliyan guda da rabi suka kasa samun makin da ake bukata. Shugaban hukumar Farfesa Ishaq Oloyede cikin hawaye ya nemi gafarar jama'a da kuma daukar alhakin lamarin.Dangane da wannan matsala, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Malam Umar Saleh Gwani masanin harkar sadarwa.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

  • Farfesa Khalifa Dikwa kan karuwar hare-haren Boko Haram a Borno

    14/05/2025 Duración: 03min

    Yayinda hare-haren ƙungiyar Boko Haram tsagin ISWAP ke ƙara tsananta musamman a Najeriya, rahotanni na cewa mayakan sun shafe ƙarshen makon jiya zuwa Litinin  da ta gabata suna kadammar da hare-hare a sassa na jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar.A tattaunawarsa da Rukayya Abba Kabara, Farfesa Khalifa Dikwa masanin tsaro a Najeriya ya ce ba abin mamaki bane yadda ‘yan ta’addar suka sauya salon kai hare-harensu. Shiga alamar sauti domin sauraron cikaken bayani.....

  • Dakta Garko akan ƙaruwar masu matsalar ƙwaƙalwa a Najeriya

    13/05/2025 Duración: 03min

    Wasu rahotanni a Najeriya na bayani akan karuwar samun mutanen dake fama da rashin lafiyar dake da nasaba da kwakwalwa, sakamakon yanayin rayuwar yau da kullum. Domin sanin tasirin matsalar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Balarabe Sani Garko na Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana. 

  • Farfesa Bello Bada kan matsalar tsaro a Arewacin Najeriya

    12/05/2025 Duración: 03min

    Gwamnonin Arewacin Najeriya tare da Sarakunan yankin sun gudanar da wani taro na musamman domin sake duba matsalolin tsaron da suka addabi yankin, a dai-dai lokacin da mayaƙan Boko Haram da ƴanbindiga ke ci gaba da hallaka jama'a ba tare da ƙaƙƙautawa ba. Bayan kammala taron, Bashir Ibrahim Idris ya tintibi Farfesa Bello Bada na Jami'ar Usman Dan Fodio da ke Sokoto. Kula latsa alamar sauti don sauraron yadda zantawarsu ta gudana akai...........

  • Dr Kassim Kurfi kan dalilan da suke sanya 'yan Najeriya ƙara talaucewa

    09/05/2025 Duración: 03min

    Dalilan da suka sanya 'yan Najeriya ke ƙara faɗawa cikin mawuyacin hali sanadiyyar talaucin da ya yi musu katutu. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin tattalin arziƙi a Najeriya Dr Kassim Garba Kurfi.Latsa alamar sauti domin sauraren tattaunawar...

  • Sanata Ali Ndume kan taron da majalisar dokokin ECOWAS tayi a Lome

    08/05/2025 Duración: 03min

    Majalisar dokokin ƙungiyar ƙasashen ECOWAS ta gudanar da taron ta a Lome da ke ƙasar Togo, wanda ya mayar da hankali kan tsadar sufurin jiragen sama a yankin. Bayan taron, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Sanata Ali Muhammed Ndume, daya daga cikin shugabannin taron. Ku latsa alamar sauti don jin cikakkiyar tattaunawar tasu.............

  • Archbishop Kaigama akan yadda ake zaɓen Fafaroma a dariƙar Katolika

    07/05/2025 Duración: 03min

    Yau manyan limaman dariƙar Katolika na duniya sama da 130 ke fara gudanar da zaɓen Fafaroma domin maye gurbin Francis da ya rasu a makon jiya.Domin sanin yadda ake gudanar da zaɓen, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Archpishop Ignatius Kaigama, daya daga cikin manyan limaman Katolika a Najeriya, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana akai. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.....

página 1 de 2