Bakonmu A Yau
Farfesa Kabir Ɗandago kan ma'aunin tattalin arzikin Najeriya a bara da kuma bana
- Autor: Vários
- Narrador: Vários
- Editor: Podcast
- Duración: 0:09:58
- Mas informaciones
Informações:
Sinopsis
Ƴan Najeriya na fatan ganin samun sauƙi a wannan shekara ta 2025, bayan da suka shiga wani yanayi na matsalin tattalin arziki a shekarar 2024 da muka yi bankwana da ita, sakamkon wasu matakai da gwamnatin shugaba Tinubu ta ɗauka, masamman janye tallafin man fetur da kuma barin naira ta ceci kanta a kasuwar canjin kuɗaɗe. Shugaban ƙasar Bola Tinubu dai ya ce gwamnatinsa za ta rage hauhawar farashi a shekarar 2025 ta hanyar haɓaka noma da tallafa wa masana'antu, danage da fatan da ƴan Najeriyar ke da shi da kuma hasashen masana dangane da farfadowa tattalin arziki a wannan shekara, Ahmad Abba ya tattauna da Farfesa Kabiru Isa Dandago na jami’ar Bayaro da ke Kano, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.