Bakonmu A Yau

Tattaunawa da Daraktan Amnesty Isa Sanusi kan yawaitar haɗarin tankar mai a Najeriya

Informações:

Sinopsis

Ƙungiyar Amnesty International ta danganta haɗrin tankin man da ya hallaka kusan mutane 100 a jihar Neja ta tsakiyar Najeriyar a matsayin talaucin da ya yiwa jama'ar ƙasar katutu,  inda daraktan ƙungiyar a Najeriyar Malam Isa Sanusi ke cewa akwai buƙatar mahukunta su sassauta matakan da suke ɗauka a lamurran da suka shafi tattalin arziƙi. Matsalar ta haɗari ko kuma gobarar tankar mai na neman zama ruwan dare a Najeriya, inda ko a baya-bayan nan aka ga yadda fiye da mutane 100 suka mutu can a jihar Jigawa sakamakon gobarar da ta tashi lokacin da suke tsaka da kalen man da ya malala akan titi bayan tuntsirewar wata tanka.Masana irin daraktan ƙungiyar ta Amnesty International mai rajin kare haƙƙin ɗan adam, Isa Sanusi na kallon talauci a matsayin babban dalilin da ke sanya mutane kai kansu ga irin wannan haɗarin wanda ke nuna buƙatar da ke akwai ga mahukunta wajen sun samar da sassauci ga jama'a don kaucewa fuskantan makamantan wannan matsaloli.Yayin wata zantawarsa da editan sashen Hausa na RFI Bashir Ibrahim I