Bakonmu A Yau

Ibrahim Wala kan bashin dala miliyan 300 da Najeriya ta ciwo daga Bankin Duniya

Informações:

Sinopsis

Bankin Duniya ya ce ya amince da buƙatar bai wa Najeriya dala miliyan 300, domin amfani da shi wajen inganta rayuwar mutanen da rikici ya raba da muhallansu a yankin arewacin ƙasar. Sanarwar Bankin ta ce za ayi amfani da kuɗaɗen ne wajen tallafawa irin waɗannan mutane da waɗanda suka basu matsuguni domin ganin sun koma masu dogaro da kan su, maimakon dogara da kayan agaji. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Ibrahim Garba Wala, ɗaya daga cikin masu fafutukar kare hakkokin jama'a a Najeriya.   Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana................