Bakonmu A Yau

Ladan Abdullahi Garkuwa kan shirin Ɗangote na rarraba mai da motocinsa sassan Najeriya

Informações:

Sinopsis

A Najeriya, ga dukkan alamu an samu rarrabuwar kawuna tsakanin dillalan man fetur, sakamakon shirin Aliko Dangote na jigilar man daga matatarsa da ke Lagos zuwa gidajen mai a sassan ƙasar. Yayin da shugabannin dillalan ke adawa da shirin Dangoten, kananan dillalan sun bayyana gamsuwar su da shirin, kamar yadda za kuji a tattaunawar Bashir Ibrahim Idris da Alhaji Ladan Abdullahi Garkuwa.