Bakonmu A Yau

Farfesa Balarabe Sani Garko kan rage farashin wanke ƙoda a wasu asibitocin Najeriya

Informações:

Sinopsis

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya amince da rage farashin wankin ƙoda daga naira 50,000 zuwa naira 12,000 a manyan asibitocin tarayya a faɗin ƙasar. Daniel Bwala, mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan Bayanan da suka shafi tsare-tsaren gwamnati ne ya bayyana hakan a shafin sada zumuntansa na X, inda ya ce matakin zai sauƙaƙa wa dubban marasa lafiya masu fama da ciwon ƙoda. An fara aiwatar da wannan mataki a manyan asibitoci kamar FMC Ebute-Metta da ke Lagos da FMC da ke Jabi a Abuja da UCH Ibadan da FMC Owerri da UMTH Maiduguri, yayin da za a ƙara wasu kafin ƙarshen shekara domin samun damar amfani da su a duk faɗin ƙasar. Sai dai da safiyar Laraba bayan rahotannin RFI, Gwamnatin Najeriya ta ɗan daidaita jerin sunayen manyan asibitocin ƙasar da za su ci gajiyar sabon tallafin domin sauƙaƙawa majinyta wanke ƙoda, inda aka ƙara asibitin koyerwa na Malam Aminu Kano da ke jihar Kano. Cikin sanarwar da ma'aikatar lafiyar ƙasar ta fitar, ta ce za'a ci gaba da ƙara wasu asibitocin ne dama sannu a hankali, amma