Bakonmu A Yau

Tattaunawa da Janar Kukasheka mai ritaya kan kama shugabannin ƙungiyar Ansaru

Informações:

Sinopsis

Gwamnatin Najeriya ta bayyana nasarar kama shugabannin ƙungiyar ƴan ta'adda da ake kira Ansaru mai alaƙa da Al'Qaeda, wadda tayi ƙaurin suna wajen kai munanan hare hare a jihohin Neja da kwara. Mai baiwa shugaban ƙasar Najeriya a kan harakokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya bada wannan sanarwar. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Tsofan kakakin runduna sojin Najeriya Janar Sani Usman Kukasheka ga kuma yadda zantawarsu ta gudana. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar hira......