Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare
Ra'ayoyin masu saurare kan ranar Malamai ta Duniya
- Autor: Vários
- Narrador: Vários
- Editor: Podcast
- Duración: 0:09:50
- Mas informaciones
Informações:
Sinopsis
A jiya ne aka gudanar da bikin ranar malamai ta duniya cikin yanayin ƙuncin rayuwa da ƙarancin albashi, musamman a wasu ƙasashen Afirka da malaman ke ɗanɗana kuɗarsu. An ware wannan rana ne, domin nuna goyon baya ga irin gudunmawar da suke bayarwa ga ci gaban rayuwar al’umma a fannoni da dama. Wanne hali malamai ke ciki a yankunanku? Shin kun gamsu da irin gudunmawar da suke bayarwa a yankunanku. Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Ku latsa alamar sauti domin sauraren shirin...