Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare

  • Autor: Vários
  • Narrador: Vários
  • Editor: Podcast
  • Duración: 3:58:54
  • Mas informaciones

Informações:

Sinopsis

Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Alumma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalinariziki, aladu da dai sauransu

Episodios

  • Ra'ayoyin Masu Saurare kan ficewar Meta daga Najeriya

    05/05/2025 Duración: 09min

    Kamfanin Meta da ya mallaki Facebook, Instagram da Whatsapp ya yi barazanar ficewa daga Najeriya bayan da aka lafta masa biyan tarar dala miliyan 290 saboda karya ƙa’ida. To sai dai gwamnatin Najeriya ta ce ko da kamfanin ya janeye daga ƙasar, to dole ne sai ya biya wannan tarar. Za mu so jin ra’ayoyinku a game da wannan takun-saka tsakanin Najeriya da kuma wannan shahrarran kamfani na sadarwa. Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.

  • Ra'ayin jama'a kan batutuwan da ke ci musu tuwo a kwarya

    02/05/2025 Duración: 09min

    Shirin ra'ayoyin masu saurare na wannan rana ta Juma'a bisa al'ada ya kan baiwa masu saurare damar fadin albarkacin bakinsu kan batutuwan da ke ci musu tuwo a kwarya. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna

  • Ra'ayoyin masu sauraro kan bikin ranar ma'aikata a sassan duniya

    01/05/2025 Duración: 08min

    Kamar dai kowace shekara, yau 1 ga watan Mayu, ita ce Ranar Ma’aikata ta Duniya, bikin da a bana ana iya cewa ana gudanar da shi ne a cikin wani yanayi na tsadar rayuwa a mafi yawan ƙasashen duniya. Abin tambayar shine, shin ko a cikin wanne yanayi ake gudanar da bukukuwan na bana, musamman a kasashen Afirka?Waɗanne irin manyan buƙatu ma'akata suke son cimma wa?Shiga alamar sauti, diomin sauraron ciakken shirin.

  • Ra'ayoyi masu saurare kan alakar Morocco da ƙasashen AES

    30/04/2025 Duración: 09min

    Bisa ga dukan alamu Maroko na ƙara samun kusanci da ƙasashen Burkina Faso, Mali da kuma Jamhuriyar Nijar a daidai lokacin da alaƙa ke ƙara yin tsami tsakanin waɗannan kaasashen da Aljeriya. Ministocin Harkokin Wajen ƙasashen uku sun ziyarci Maroko tare da ƙulla yarjejeniyar da ke ba su damar yin amfani da tashoshin ruwa ƙasar, alhali ba ɗaya daga cikinsu da ke da iyaka da Marokon.Ko yaya ku ke kallon wannan alaƙa tsakanin Maroko da AES, yayin da suka juya wa makociyarsu Aljeriya baya?Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.

  • Yadda ake zargin gwamnatin Najeriya da shaƙe wuya ƴan adawa

    29/04/2025 Duración: 10min

    Shirin ra'ayoyin ku masu saurare na wannan rana ya mayar da hankali ne kan yadda wasu fitattun mutane mambobin kungiyar farar hula a Najeriya suka nuna takaicinsu kan yadda gwamnatin mai ci ke neman mayar da kasar tsarin jam'iyya daya. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Oumarou Sani

  • Ra'ayoyin masu sauraren shirye-shiryen RFI

    25/04/2025 Duración: 10min

    A duk ranar Juma'a, RFI Hausa na bai wa jama'a damar tofa albarkacin bakinsu kan abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya kama daga siyasa, tattalin arziki, zamantakewa, harkokin yau da kullum da dai saurarensu. Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan rigakadin cutar Polio a Najeriya

    24/04/2025 Duración: 09min

    Yayin da a yau aka ƙaddamar da makon rigakafi a duniya, Hukumomi a Najeriya da kuma Unicef, sun yi gargaɗin cewa yanzu haka nau’ukan cutar shan’inna har guda 17 da suka yaɗu a cikin jihohi 8 na ƙasar. Wannan dai babban ƙalubale ne ga sha’anin kiwon lafiya, bayan da aka shelanta kawo ƙarshen cutar tun 2020.Shin ko meye dalilan sake ɓullar wannan cuta a Najeriya?Waɗanne matakai ya kamata a ɗauka domin shawo kanta?Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin masu saurare.

  • Halin da wasu ƴan Najeriya suka shiga bayan da kamfanin CBEX ya tsere da kudadensu

    17/04/2025 Duración: 09min

    Shirin ra'ayoyin masu saurare na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda wani kamfanin hada-hadar kudi ta Internet a Najeriya mai suna CBEX ya tsere da kudaden jama'a. Danna alamar sauarre domin jin cikakken shirin tare da Nasiru Sani

  • Yadda ƴan Najeriya suka shiga halin fargaba a game da yiwuwar ambaliyar ruwa a jihohi 30

    16/04/2025 Duración: 10min

    Shirin ra'ayoyin masu saurare na wannan mako ya mayar da hankali ne kan gargaɗin gwamnatin Najeriya na yiwuwar samun ambaliyar ruwa a jihohi 30 a daminar bana. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Abida Shu'aibu.

  • Gagarin da ilimin yara mata ya shiga sakamakon ta'addanci a Najeriya

    15/04/2025 Duración: 10min

    Shirin ra'ayoyin masu saurare na wannan rana ya mayar da hankali ne kan yadda kungiyoyin ta'addanci ke kawowa ilimin yara mata tsaiko a Najeriya. Danna alamar sauarre don jin cikakken shirin tare da Nasiru Sani.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwan da ke ci musu tuwo a ƙwarya

    14/03/2025 Duración: 10min

    Yau ta ke ranar jin ra'ayoyin ku masu saurare kan batutuwan da ke ci muku tuwo a ƙwarya, kama daga fannin siyasa, ilimi, lafiya, tattalin arziƙi da dai sauransu. Latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi...

  • Kan yadda EFCC ta kwato Naira tiriliyan guda daga hannun ɓarayin gwamnati

    11/03/2025 Duración: 09min

    Hukumar Yaƙi da Rashawa a Najeriya EFCC, ta ce a cikin shekarar ta 2024 da ta gabata, ta yi nasarar ƙwato kusan Naira tiriliyan ɗaya daga hannun barayi da masu handame dukiyar al’umma. EFCC ta ce ko a gaban kotu ma, ta samu nasarori sama da sau dubu huɗu akan masu cin rashawa da kuma ƴan damfara cikin shekarar da ta gabata.Abin tambayar shine, ko aikin hukumar na gamsar da 'yan Najeriya?Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakakken shirin.

  • Kan yadda direbobin manyan motoci ke fuskantar kisa daga 'yan awaren Biafara

    04/03/2025 Duración: 10min

    Ƙungiyar direbobin motoci a Najeriya, ta buƙaci mahukunta su ɗauki matakan kawo ƙarshen kisan da ƴan awaren Biafra ke yi wa direbobin manyan motoci a duk lokacin da suke ratsa yankin kudu maso gabashin ƙasar. Ƙungiyar ta ce an kashe mambobinta sama da 50, kuma 20 daga cikinsu an kashe su ne a shekarar 2024, sannan aka kwashe kayayyaki da kuma ƙona motocinsu.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwan da ke ci muku tuwo a ƙwarya

    28/02/2025 Duración: 10min

    A yau Juma'a kamar yadda aka saba, masu sauraro ko kuma bibiyarmu a shafukan sada zumunta, kan aiko da saƙonnin ra'ayoyi kan batutuwa da dama, kama daga wanda ke ci musu tuwo a ƙwarya a fannoni daban-daban na rayuwa, da kuma fannin tattalin arziki, da tsaro, da lafiya, da siyasa da sauransu.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan yawaitar masu ta'ammali da ƙwayoyi a Arewacin Najeriya

    27/02/2025 Duración: 10min

    Aƙalla 40% na mazauna yankin arewa maso yammacin Najeriya ne ka tu’ammuli da miyagun ƙwayoyi, kuma kusan 28 cikin ɗari suna zaune ne a jihar Kaduna kamar dai yadda rahoton hukumomin da yaƙi da wannan matsala ya nuna.  Hakazalika, mutum 1 cikin 7 a yankin arewa maso yammacin ƙasar suna tu’ammali da miyagun ƙwayoyin a cewar rahoton.Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin...

  • Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa mabanbata

    21/02/2025 Duración: 09min

    A yau Juma'a kamar yadda aka saba, masu sauraro ko kuma bibiyarmu a shafukan sada zumunta, kan aiko da saƙonnin ra'ayoyi kan batutuwa da dama, kama daga wanda ke ci musu tuwo a ƙwarya a fannoni daban-daban na rayuwa, da kuma fannin tattalin arziki, da tsaro, da lafiya, da siyasa da sauransu. Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin...

  • Ra'ayoyin masu saurare kan tarar da za a ci masu satar lantarki a Najeriya

    20/02/2025 Duración: 09min

    Hukumar Ƙayyade Farashin Wutatar Lantarki a Najeriya, sanar da sabon tsarin biyan tara a kan waɗanda ke satar makamashin lantarki a ƙasar. Tarar ta kama daga Naira dubu 100 zuwa dubu 300 daidai da irin salon da mutum ya yi wajen sada gidansa da wannan makamashi.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan saukar farashin kayan abinci a Najeriya

    19/02/2025 Duración: 09min

    Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa a Najeriya, ta ce farashin kayan abinci ya sauka a cikin watan Janairun da ya gabata da 10% idan aka kwatanta da na wata Disamba. To waɗannan dai bayanai da hukuma ta fitar, saboda haka za mu so jin ra’ayoyinku a game da wannan rahoto.Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin tare da Abida Shu'abu Baraza...

  • Ra'ayoyin masu saurare kan kashe maƙudan kuɗaɗe don inganta lantarki a Najeriya

    18/02/2025 Duración: 10min

    Alƙalumma na nuni da cewa a cikin shekaru 10 da suka gabata, an kashe aƙalla Naira Tiriliyan 7 da bilyan 200 a matsayin tallafi da nufin inganta sanar da wutar lantarki a Najeriya. To sai dai a zahirin ana cewa har yanzu wannan ɓangare na ci gaba fama da matsaloli masu tarin yawa, yayin da a ɗaya ɓangare farashin wutar ya ninka ninkin ba ninkin.

  • Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa mabanbanta

    07/02/2025 Duración: 11min

    A yau Juma'a kamar yadda aka saba, masu sauraro ko kuma bibiyarmu a shafukan sada zumunta, kan aiko da saƙonnin ra'ayoyi kan batutuwa da dama, kama daga wanda ke ci musu tuwo a ƙwarya a fannoni daban-daban na rayuwa, da kuma fannin tattalin arziki, da tsaro, da lafiya, da siyasa da sauransu. Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyi mabanbanta...

página 1 de 2