Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare

Ra'ayoyin masu saurare game da dambarwar ƙungiyar PENGASSAN da Ɗangote

Informações:

Sinopsis

A Najeriya ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin matatar Dangote da kungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas wato PENGASSAN. Tun daga lokacin da matatar Dangote ta fara aiki kawo yanzu, an samu takaddama irir-iri daga kungiyoyin da ke da alaka da man fetur da kuma iskar gas. Ko me yasa takun saka tsakanin Dangote da masu ruwa da tsaki a harkar mai, yaki ci yaki cinyewa? Me ku ke ganin ummul aba’isin wannan dambarwa da take bullowa daga kusurwa-kusurwa, wanda ake ganin zai haifar da tashin farashin mai a Najeriya? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai........ Ku latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyin na ku.....................