Wasanni

  • Autor: Vários
  • Narrador: Vários
  • Editor: Podcast
  • Duración: 3:59:45
  • Mas informaciones

Informações:

Sinopsis

A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.

Episodios

  • Gudummawar da cibiyoyin horar da matasa wasan kwallon ƙafa ke bayarwa a Najeriya

    18/11/2024 Duración: 10min

    Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya yi duba ne kan irin gudummawar da cibiyoyin horar da matasa wasan kwallon ƙafa ke bayarwa wajen zakulo matasan ƴan wasa da horar da su a Nigeria. Wannan dai wani bangare ne na gudummawarsu ga ci gaban wasan kwallon ƙafa a Nigeria, tsofin ƴan wasan tawagar Super Eagles na ƙasar, sun fara kafa cibiyoyi masu zaman kan su, da su ke zakulowa tare da horar da matasa don yin fice a harkar ta kwallon kafa. Irin wadannan cibiyoyin horar da matasa wasan na kwallon kafa da a turance ake kira Football Academy, kan shiga birane da karkara don tuntubar ƙanana da matsakaitan club-club, domin samun ƴan wasan daga wajen su da za a yi rijistarsu a wannan cibiya.Pascal Patrick, tsohon ɗan wasan Super Eagles kuma shugaban Hukumar kwallon kafa ta NFA a jihar Bauchi kana co-odinetan tawagar Super Eagles na Nigeria, na daya daga cikin tsofaffin ƴan wasan ƙasar da suka kafa irin wannan cibiya a jihar Bauchi.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.......

  • Yadda cece-kuce ya mamaye kyautar Ballon d'Or ta 2024

    04/11/2024 Duración: 09min

    Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan makon ya yi dubi ne akan yadda aka gudanar da bikin bada kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2024.

  • Hukuncin da CAF ta yi kan danbarwar Najeriya da Libya da kuma wasan El-Clasico

    28/10/2024 Duración: 09min

    Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon yayi duba ne kan yadda wasan El-Clasico ya gudana da kuma hukuncin da Hukumar Kwallon Ƙafar Afrika CAF tayi kan danbarwar Najeriya da Libya. A ƙarshen mako ne dai kwamin ladaftarwa na hukumar CAF, ya zartar da hukuncin cewa Najeriya ce tayi nasara da ci 3 da nema kan Libya, tare da tarar dala dubu 50. Haka nan shirin ya duba yadda wasan El-Clasico ya gudana tsakanin Real Madrid da Barcelona da aka yi a ƙarshen mako.

  • Danbarwar da ta ɓarke kan wasa tsakanin Najeriya da Libya

    21/10/2024 Duración: 10min

    Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan danbarwar da aka samu tsakanin Najeriya da Libya. A makon daya gaba ne dai aka fara kai ruwa rana tsakanin bayan da tawagar Super Eagles ta Najeriya ta yi tattaki zuwa Libya don karawa da takwaransu ta ƙasar a wasa na biyu na neman gurbin zuwa gasar lashe kofin Afrika da za ayi a Morocco a shekara mai zuwa. Wannan al’amari dai ya haifar da cece-kuce a duniyar kwallon ƙafar, ganin yadda Super Eagles ta zargi hukumomin kwallon ƙafar Libya da yin watsi da su a filin jirgin sama ba tare da ance kuci kanku ba.Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh.....

página 2 de 2