Sinopsis
Muna gabatar muku da shirye-shirye masu ayatarwa da suka shafi al´adu da zamantakewa tsakanin al´ummomi da mabiya addinai daban-daban da nufin kyautata tsarin zamantakewa da fahimtar juna ta hanyar tuntuar juna da shawarwari tsakani ba tare da nuna fifiko akan wani ba.
Episodios
-
Taba Ka Lashe: 02.03.2022
08/03/2022 Duración: 09minKo har yanzu ana amfani da wakokin gargajiya da kayan kidan harshen Hausa a kasar Hausa? Shirin Taba Ka Lashe.
-
Taba Ka Lashe: Rayuwar Musulmi da Kirista
15/02/2022 Duración: 09minMusulmi da Kirista a Jihar Filaton Najeriya na zaune a unguwani dabam-dabam sabanin yadda a baya al'ummomin biyu ke zaune wuri guda suna cudanya.
-
Taba Ka Lashe 02.01.2022
08/02/2022 Duración: 09minShirin na wannan lokaci ya yi nazari ne a kan kirari. Ya al'adar kirari take a kasashen Afirka?
-
Taba Ka Lashe: 26.01.2022
01/02/2022 Duración: 09minShirin na wannan lokaci ya ziyarci jihar Osun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya, inda ya gano wani Masallaci da ya kwashe shekaru aru-aru.
-
Taba Ka Lashe: 29.12.2021
04/01/2022 Duración: 09minKo kun san su wanene mafarauta da 'yan tauri da kuma yadda suke samun taurin? Ku saurari Shirin Taba Ka Lashe.
-
Taba Ka Lashe: 22.12.2021
28/12/2021 Duración: 10minShirin ya duba yunkurin farfardo da wata sarautar gargajiya ta kabilar Abzinawa a garin Afess na jahar Agadez a Nijar.
-
Taba Ka Lashe: 15.12.2021
21/12/2021 Duración: 09minAn gudanar da bikin nadin sababbin sarautu, a masarautar Hausawan Turai. Karin bayani cikin Taba Ka Lashe.
-
Taba Ka Lashe: 08.11.2021
14/12/2021 Duración: 09minMata na taka muhimmiyar rawa, wajen magance rikice-rikicen kabilanci da na addinai da makamantansu. Shirin Taba Ka Lashe.
-
Taba Ka Lashe: 24.11.2021
30/11/2021 Duración: 09minKo kun san yadda mabiya darikun Sufaye ke ziyara Kushewar Waliyai a Maroko? Shirin Taba Ka Lashe.
-
Taba Ka Lashe
16/11/2021 Duración: 09minWurin da ake tsugune da daruruwan mata da ake zargi da aikata maita a wata cibiya ta musamman da ake wa lakabi da "Sansanin mayu” a arewacin Ghana.
-
Taba Ka Lashe: 27.10.2021
02/11/2021 Duración: 09minA duk ranakun 12 ga watan Rabi'ul Auwal na ko wacce shekara, al'ummar Musulmi a fadin duniya kan yi bukukuwan tunawa da ranar haihuwar Manzon Allah Annabi Muhammad (SAAW). A wannan shirin mun yi nazarin yadda aka gudanar da bukukuwan na bana a jihar Kano da ke Najeriya.
-
Taba Ka Lashe 22.09.2021
28/09/2021 Duración: 09minYadda zamani ke shirin gusar da al'adun gargajiyan jahar Gaya a jamhuriyar Nijar. Latsa kasa don jin cikakken shirin.
-
Taba Ka Lashe: 15.09.2021
21/09/2021 Duración: 10minAmfani da ahnnun hagu, halitta ce da daga Allah. Sai dai wasu na fuskantar kalubale sakamkon wasu al'adu da ma addinai. Ku saurari shirinmu na Taba Ka Lashe.
-
Taba Ka Lashe: 01.09.2021
07/09/2021 Duración: 09minKo kun san yadda kabilar Igbo da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, ke bikin binne gawa? Shirin Taba Ka Lashe.
-
Taba ka lashe 04.05.21
31/08/2021 Duración: 09minAl'adar wasan kara a yankin Damagaram na Jamhuriyar Nijar wanda matasa ke yi a lokacin kaka bayan girbin amfani gona
-
Taba Ka Lashe: 11.08.21
24/08/2021 Duración: 10minKo kun san cewa akwai fadar Hauasawa har ma da sarkinsu a Turai? Shirin Taba Ka Lashe ya yi nazari kan batun wannan sarauta.
-
Taba Ka Lashe: 04.08.2021
10/08/2021 Duración: 09minKo kuna da masaniya kan yadda al'adar wasan kara ke gudana a jihar Damagaram da ke Jamhuriyar Nijar? Shirin Taba Ka Lashe
-
Taba Ka Lashe: 21.07.2021
27/07/2021 Duración: 09minShadi, dadaddiyar al'ada ce ta Fulani da aka fi amfani da ita wajen neman aure. Sai dai a yanzu al'amura sun sauya. Ko ya al'adar ta shadi take gudana a yanzu? Shirin Taba Ka Lashe.
-
Taba ka Lashe 21.07.2021
20/07/2021 Duración: 09minAl'adar Sharo na fulani wata dadaddiyyar al'ada ce mai muhimmanci ga fulani wacce tun shekaru masu yawa suke yin ta musamman domin hada aure tsakanin samari da yan mata.
-
Taba Ka Lashe: 07.07.2021
13/07/2021 Duración: 09minKo kun san irin baiwar da aka yi ittifakin cewa 'yan tagwaye ko kuma 'yan biyu na da su a kasashen Hausa masu tarin al'adu? Shirin Taba Ka Lashe.