Sinopsis
Shirin yakan diba kasuwancida tattalin arizikin kasashen duniya ya ke ciki. Shirin yakan ji sabbin dubaru da hajojin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masanaantu dangane da halin da suke ciki.
Episodios
-
Yadda matan Arewacin Najeriya ke ƙara yin tasiri a kasuwancin jihar Lagos
28/05/2025 Duración: 13minShirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmad Abba ya mayar da hankali ne kan babban taron da ƙungiyar Matan Arewa ƴan kasuwa mazauna Lagos da ke kudancin Najeriya su ka yi a birnin Lagos, wanda ya mayar da hankali kan karfafawa mata gwiwa kan harkokin kasuwanci da bunkasa tattalin arzikinsu.
-
Yadda karancin wutan lantarki ke kokarin durkusar da masu masana'antu a Najeriya
14/05/2025 Duración: 10minShirin Kasuwa A kai Miki Dole na wanan makon tare da Ahmed Abba ya yi duba kan irin girman asarar da masau kamfanoni su kace sun tafka saka makon matsalar karancin wutan lantarki da ake fama da ita musamman a arewacin kasar. Ku shiga alamar sauti domin jin cikakken shirin......
-
Yadda gobara ta haddasa mumuna asara ga 'ƴan kasuwar Taminus ta Jihar Filato
07/05/2025 Duración: 10minShirin Kasuwa akai Miki Dole na wanan makon tareda Ahmed Abba , ya mayar da hankali kan asarar sama da Naira biliyan ɗaya da ƴan kasuwar Taminus na birnin Jos suka tafka sakamakon konewar wani bangare na babbar kasuwar ta jihar Filato dake Najeriya. Ku latsa alamar sauti domin sauraron karin bayani.......