Sinopsis
Kawo aladu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jamaa masu aladu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.
Episodios
-
Irin rawar da ya kamata masarautu su taka wajen kawo sauye-sauyen da suka kamata
04/06/2024 Duración: 10minShirin al'adun gargajiya na wannan mako ya yi duba ne a kan muhimancin sarakunan mu da kuma irin rawar da za su iya takawa a wannan lokaci da ake fuskantar sauye-sauye a fanoni da dama. shirin ya tattauna da sarakunan masarautun Macina da kuma ta Nupe. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.........
-
Koken Jama'a a kan yadda hukumomi ke yi wa abubuwan tarihi rikon sakainar kashi
21/05/2024 Duración: 10minShirin al'adun gargajiya na wannan mako ya yi duba ne a kan yadda Jama'a ke koken game da rikon sakainar kashi da hukumomi ke yi wa abubuwan tarihi, kamar Makon jiya yau ma shirin ya yi tattaki ne har Kanon Dabo da ke tarayyar Najeriya, inda ya tattauna da shugaban kwamitin raya Al'adun Gargajiya na Majalisar dokokin Jihar, Hon. Sarki Aliyu Daneji.Ku latsa alamar sauti don jin yadda shirin ya kasance....
-
Yadda Maza da Mata suka rungumi sana'ar Rini a Kano da ke Najeriya
14/05/2024 Duración: 10minShirin al'adun gargajiya na wannan mako ya yi tattaki ne har Kanon Dabo da ke tarayyar Najeriya, inda ya yi duba a kan yadda Maza da Mata suka rungumi sana'ar Rini a Karofin Kofar Mata wadda ke da dogon Tarihi.Shirin ya samu zarafin tattauna wa da Baballiya Hamisu, wanda shi ne mai magana da yawun Marinar ta Kofar Mata.
-
Yadda tsadar rayuwa ke barzana ga Maroka da Sankira a Jamhuriyar Nijar
26/03/2024 Duración: 10minShirin al'adun gargajiya na wannan mako ya duba yadda jama'a a Maradi suka koma amfani da ruwan randa a maimakon kankara lokacin azumin watan Ramadana, saboda tsadar kankarar. Akwai mu dauke da yadda Maroka da kuma Sankira ke fuskantar barazana a sakamakon tsadar rayuwa.Dannan alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Abdullahi Isa.