Sinopsis
Shirin Lafiya yana tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jamaa, Sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Talata da yamma.
Episodios
-
Matakan da ya kamata a ɗauka yayin kai ɗaukin gaggawa a lokacin faruwar haɗari
21/04/2025 Duración: 10minShirin Lafiya Jari ce a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan matakan da ya kamata mutane su riƙa ɗauka gabanin kai ɗaukin gaggawa a lokacin afkuwar haɗari ko ibtila'i, waɗanda rashinsu a wasu lokutan ke kaiwa ga asarar rayuka ko kuma haddasa gagarumar illa ga mutanen da haɗarin ya rutsa da su. Shirin ya shawarci jama'a game da samun ilimin iya kai ɗaukin gaggawa don kaucewa haddasa matsala ba tare da sani ba ga mutanen da ake ƙoƙarin ceton rayuwarsu.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
Ana samun ƙaruwar masu kamuwa da cuta mai karya garkuwar jiki a Ghana
14/04/2025 Duración: 10minShirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan ƙaruwar masu kamuwa da cuta mai karya garkuwar jiki ko kuma HIV AIDS ko sida tsakanin matasan Ghana a shekarun baya-bayan nan, wadda masana ke ɗora alhakin yawaitarta kan rashin ɗaukar matakai. Wannan ƙaruwar alƙaluma na zuwa a dai dai lokacin da duniya ke ganin ƙarancin magunguna rage kaifin cutar sakamakon matakin Amurka na zaftare tallafin da ta ke bayarwa ƙarƙashin ƙungiyar USAID.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shiri.
-
Mutane na ɓoye cutukan ƙwaƙwalwa saboda fargabar alaƙantasu da hauka
24/03/2025 Duración: 10minShirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya yi duba na musamman kan cutuka ko kuma lalurar ƙwaƙwalwa, dama rabe-rabenta baya ga nazarin yadda mutane ke ɓoye irin wannan lalura saboda kunyar kar a alaƙanta su da ciwon hauka. Alƙaluman hukumar lafiya ta duniya WHO a shekarar 2017 sun nuna cewa kashi 19 na yawan al’ummar duniya na fama da matsalar ƙwaƙwalwa walau a babban mataki ko kuma a mataki na ƙasa, matsalar da kuma bayanan hukumar ke cewa yafi tsananta a ƙasashe masu tasowa.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
An samu ɓullar cutar sankarau a wasu jihohin arewacin Najeriya
17/03/2025 Duración: 10minShirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon ya mayar da hankali ne akan cutar sankarau, wanda ke yin ƙamari a cikin yanayi na zafi da ake ciki, musamma a ƙasashenmu na nahiyar Afrika. Tuni aka samu ɓullar cutar sankarau a sassa daban-daban na Najeriya inda ta kashe gomman mutane a jihohin Kebbi da Sokoto, wadda aka bayyana ta da annoba. Masana a ɓangarorin lafiya da kuma yanayi, na ci gaba da gargaɗi kan yiwuwar ɓullar tarin cutuka sakamakon tsananin zafin da ake fuskanta a wasu daga cikin jihohin Najeriya, a wani yanayi da ake ci gaba da azumin watan Ramadana,, wannan shi ne maudu’in da shirin lafiya jari ce na wannan mako zai mayar da hankali akai sai ku biyomu.