Sinopsis
Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-dabam a duniya, tare da nazari ga irin ci gaban da aka cim ma wajen binciken kimiya da fasaha da ke naman saukakawa Danadam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Biladam. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe.
Episodios
-
Yadda za'a koya wa yara iya karatu tun daga matakin farko a Najeriya
04/02/2025 Duración: 10minShirin ilimi hasken rayuwa na wannan lokaci ya mayar da hankali kan yadda za'a bi ƙa'idoji da hanyoyi domin koya wa yara iya karatu a matakin farko a Najeriya. Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin...
-
Gasar HIFEST karo na bakwai a Najeriya
28/01/2025 Duración: 10minShirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako, ya yi duba ne, kan yadda wata kungiya a Najeriya, ke karfafa gwiwar daliban sakandire kan yadda za su bayyana baiwar da suke da ita, musamman a bangaren ilimin fasaha.
-
Mahimmancin kwalejojin fasaha a Najeriya wajen bunƙasar ɓangaren ilimin kimiyya
24/12/2024 Duración: 10minShirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan makon ya yi nazari ne kan mahimmancin kwalejojin fasaha na Najeriya ga bunƙasar ɓangaren ilimin kimiyya da fasaha a ƙasar, da kuma kalubalen da suke fuskanta a halin yanzu, sai kuma duba hanyoyin da za a bi don farfaɗo da martabarsu. Ku latsa almar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman............