Sinopsis
Shirin yakan diba kasuwancida tattalin arizikin kasashen duniya ya ke ciki. Shirin yakan ji sabbin dubaru da hajojin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masanaantu dangane da halin da suke ciki.
Episodios
-
Yadda aka samu hauhawan farashin kayan abinci a kudancin Najeriya
18/12/2024 Duración: 10minShirin kasuwa akai miki dole zai mayar da hankali ne kan yadda farashin kayan abinci ya ke hauhawa a Najeriya, daidai lokacin da ake shirye shiryen bukukuwan Kirsimeti, musamman a kudancin ƙasar, inda a halin yanzu farashin buhun albasa yakai sama da ₦320,000 yayin da buhun shinkafa ƴar gida yakai ₦120,000. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba..........
-
Bankin duniya ya ayyana Najeriya a matsayin ƙasa ta uku wajen cin bashi a duniy
27/11/2024 Duración: 10minWani rahoton Bankin Duniya ya nuna cewa Najeriya ce ƙasa ta uku a yawan basususun kasashen ketare, bayan da ta ƙarbi sama da dalar Amurka biliyan 16.5 kwankwacin naira Triliyan 27 da biliyan 700. Da wannan matsayi Najeriya ta na biye ne da ƙasashen Bangladesh mai matsayi na ɗaya da Pakistan ta biyu a yawan basussuka a duniya.Sabon ranceHakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da majalisar dattawan najeriyar ta sahalewa shugaba Tinubu karbo sabon rancen naira Tiriliyan 1 da biliyan 700, duk da ikirarin ƙasar na samun ƙudin haraji mai yawa daga hukumar kwastom da sauransu.Yawan basussukaBayaga bankin duniya duniya, jummular basussukan da Najeriya ta ƙarbo ya kai naira triliyan 138, wanda hasashe ma ke cewa zai kai dala biliyan 45 kafin karshen wannan shekara ta 2024.
-
Faɗuwar darajar Naira na shafar kasuwancin dabbobi a iyakar Najeriya da Nijar
07/11/2024 Duración: 10min'Shirin Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya duba yadda harkokin kasuwanci ke tafiya a kasuwar dabbobi ta ƙasa da ƙasa da ke Maigatari ta Jihar Jigawa, wato kan iyakar Najeriya da Nijar, da kuma jin irin ƙalubalen da kasuwar ke fuskanta. Kasuwar ta Maigatari wadda ke iyakar Najeriya da Nijar na daya daga cikin manyan kasuwannin dabbobi a yankin arewacin Najeriya, domin ana sayar da nau'ikan dabbobi da suka hadar da shanu, raƙuma, dawaki, tumaki, awaki da jakkai sama da miliyan biyu a ranakun Alhamis din ko wanne mako, kuma yan kasuwa daga sassan Najeriya, Nijar da kuma Mali na zuwa a duk mako.
-
Yadda ta kaya a taron bunkasa tattalin arziki ta kafofin internet a Najeriya
16/10/2024 Duración: 10minShirin kasuwa a kai miki dole na wanna mako ya yi tattaki zuwa taron masu ruwa da tsaki ne a fannin bunkasa tattalin arziki ta kafofin internet wadda a turance ake kira digital economic wanda aka gabatar a jihar Lagos a tarayyar Najeriya.
-
Yadda ƴan kasuwa tsakanin Najeriya da Kamaru ke fuskantar kalubalen rashin hanya
09/10/2024 Duración: 10minShirin Kasuwa Akai Miki Dole na wannan makon ya maida hankali ne kan hada-hadar kasuwaci tsakanin Najeriya da makwabciyarta Kamaru, da irin kalubalen da ƴan kasuwar Kamaru da diribobi daga ƙasashen biyu ke fadi tashi a kan iyakokin ƙasashen biyu. Ƴan kasuwar ƙasashen biyu na amfana da juna, a wasu manyan hanyoyin 10 da a hukumance aka san da su da suka hada na mota da kuma ruwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba......
-
Najeriya: Yadda ambaliyar ruwa ta kassara tattalin arzikin al'ummar Maiduduri
25/09/2024 Duración: 10minShirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya leka ne jihar Barno da ke arewa maso gabashin Najeriya, inda ya mayar da hankali kan tasarin tattalin arziki da ambaliyar baya-bayan nan ya haifarwa jihar da ma al'ummarta. Makonni biyu kenan tun bayan mummunar ambaliyar ruwa da ta afkawa wasu anguwannin birinin maiduguri na jihar Borno da kewaye, a ranar 10 ga wannan watan Satumba, iftila'in da ya haifar da asarar rayuwa da dukiyoyi mai tarin yawa, tare da lalata gidaje da kasuwanni, inda mutane da yawa suke nemi mafaka a wasu sansanonin yan gudun hijara na wucin gadi, yayin da wasu ke gararamba a kan tituna.
-
Ƙarin farashin man fetur ya sake jefa iyalai da dama a halin tsaka mai wuya
11/09/2024 Duración: 10minShirin kasuwa a kai miki dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya mayar da hankali kan matsi da tsadar rayuwa da kuma yadda wannan matsala ta jefa kaso mai yawa na magidantan Najeriya a halin tsaka mai wuya, matsalar da ke da nasaba da sabbin manufofin gwamnati ciki har da ƙarin farashin man fetur.
-
Yadda gwamnan CBN ya kashe naira biliyan 60 wajen siyen motocin alfarma
04/09/2024 Duración: 10minShirin "Kasuwa akai miki dole" tare da Ahmed Abba a wannan makon ya mayar da hankali ne kan matakin Babban Bankin Najeriya CBN na sayen motocin sulke na katsaita guda shida da ƙudin su ya haura naira biliyan 60, wanda gwamnan bankin da mataimakansa za su yi amfani da su, daidai lokacinda ƴan ƙasar ke fama da tsananin tsadar rayuwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba......
-
Tasirin da tsarin musayar zinare ga makamashi ya yi ga tattalin arzikin Ghana
28/08/2024 Duración: 09minShirin kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya waiwayi shirin gwamnatin Ghana na ban gishiri in baka manda a musayar zinare da man fetir, duk dai a ƙoƙarin da ƙasar ke yi na haɓaka tattalin arziƙinta. Tun a bara ne gwamnatin na Ghana ta ƙaddamar da tsarin na ban gishiri in baka manda, wanda ta ƙarbi tan dubu 40 na man disel da ƙudinsu ya kai dala miliyan 40 wajen musanya da zinare da ƙasar ke da arzikinsa.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...
-
Masu sana'ar kifi a Najeriya sun koka kan tsadar abincin kiwo
21/08/2024 Duración: 10minShirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya duba yadda kasuwancin kifi a Najeriya ya ke neman ya gagari masu sana’ar saboda tsadar abincin da ake kiwon kifi da shi da farashin sa ya ƙaru, lamarin da ke barazana musamman ga ƙanana da matsakaitan ƴan kasuwa a fannin. Farashin buhun abincin kifi ya tashi daga N18,000 a shekarar 2023 zuwa N36,000 a wannan shekarar, wanda ya nuna karuwar kashi 100 cikin 100 a fadin Najeriya.Wannan al’amari ya yi kamari a yankin Neja Delta da suka yi kaurin suna a noman kifi.
-
Najeriya ta yi asarar sama da naira triliyan 5 a zanga-zangar kwanaki 10
14/08/2024 Duración: 09minShirin Kasuwa A kai miki Dole na wannan makon tare da Ahmad Abba ya tattauna irin asarar da aka yi a Najeriya sakamakon zanga zangar kwanaki 10 da ƴan ƙasar suka yi domin nuna adawa da tsadar rayuwa da rashin shugabanci na gari. Ministar masana’antu da Kasuwanci da kuma zuba jari na kasar Dr. Doris Uzoka Anite ta ce, alkakuma da suka tattara na wucin gadi, sun nuna cewa Najeriya ta yi asarar naira biliyan 500 a duk rana ta Allah yayin zanga-zangar, bayaga dukiyar da aka barnata ta hanyar kone-kone ko sata da makamanci hakan da takai naira biliyan 52, kamar yadda ta wallafa a shafinta na X.
-
Yadda basuka su ka yi wa ƙasar Ghana katutu a cikin shekara guda
07/08/2024 Duración: 09minA yau shirin zai waiwai kasar Ghana, inda basusukan da ake bin kasar ya karu da dala biliyan 47.4 / Cidi biliyan 658.6 a cikin watanni biyun farko na shekarar 2024.Babban Bankin ƙasar ta Ghana ne ya fitar da wadandan alkaluma cikin wani rahoton da ya fitar na taƙaitaccen Bayanan Tattalin Arziki da Kuɗi na watan Mayun shekarar 2024. A cewar babban bankin na Ghana, bashin da ake bin ƙasar ya karu ne zuwa Cidi biliyan 658.6 a watan Fabrairun wannan shekarar, tsabanin Cidi biliyan 611.2 da yake a ƙarshen shekarar 2023.
-
Yadda Najeriya ke fuskantar tashin farashin kayayyaki mafi muni cikin shekaru 30
24/07/2024 Duración: 10minA wannan mako shirin ya mayar da hankali ne kan wani rahoto da hukumar ƙididigar ta Najeriya ta fitar cewa an sake samun hauhawan farashin kayayyaki wanda ƙasar ba ta taɓa gani ba cikin shekaru 30, daidai lokacin da gwamnatin ƙasar ke faɗi tashin kawowa al’umma sauƙi kan tsananin rayuwa da suke ciki, tare da amincewa da Naira dubu 70 a amatsayin mafi ƙarancin albashin ma’aikata. Shin ko hakan zai kawo sauƙi kan halin da ake ciki a ƙasar? Kuna iya latsa alamar sauti don jin amsar wannan tambaya tare da masana ta cikin shirin...
-
Gwamnatin Najeriya za ta yi odan abinci daga waje saboda tsadar rayuwa a ƙasar
17/07/2024 Duración: 10minShirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' a wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan sabon matakin gwamnatin Najeriya na sahale shigo da muhimman kayan abinci kamar su shinkafa da wake da alkama da masara ba tare da biyan ƙudin fito ba har tsawon watanni 5, domin rage tasirin tsaɗar kayan abinci da ƴan ƙasar ke fama da shi tun bayan ɗarewar shugaba Bola Ahmed Tinubu mulki a bara. A wani taron manema labarai da ya kira wannan Litinin, ministan noma da samar da abinci na Najeriya, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana sabon matakin, inda ya ce shugaba Tinubu ya amince da janye ƙudin fito da kuma haraji kan muhimman kayan abincin ne har na tsawon kwanaki 150, domin wadatuwar kayan a Najeriya.Sanarwar ta ce baya ga janye ƙuɗin fito ga ƴan kasuwa masu bukatar shigo da kayan abinci, ita kanta gwamnatin tarayya za ta shigo da alkama da Masara kimanin tan dubu 250 kowanensu, domin bai wa kamfanoni jihohi da ke sarrafa su.
-
Yadda gwamnatin Nijar ta saukaka farashin shinkafa ga al'ummar kasar
03/07/2024 Duración: 09minShirin 'Kasuwa akai Miki Dole na wannan makon ya maida hankali kan yadda gwamnatin Jamhuriyar Nijar, ta fara saidawa talaka shinkafa a farshi mai rahusa, domin saukakawa ƴan kasar radadin matsin tattalin da suke ciki sakamakon juyin mulki da sojoji suka yi. A ranar 26 ga watan Yunin da ya gabata gwamnatin Nijar ta hannun ma’aikatar kasuwanci ta kaddamar da wannan shirin, inda ake sayar da buhu mai nauyin kilo 23 kan jaka 13 da rabi maimakon jika 17 zuwa jika 19 da ake sayar da shi a a wasu wurare.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba......
-
Lokaci ya yi da Najeriya za ta rinka fitar da manja kasashen waje - Ƙungiyoyi
26/06/2024 Duración: 09minShirin 'Kasuwa akai Miki Dole na wannan makon ya maida hankali da kan kiranda wasu kungiyoyi suka yi wa gwamnatin Najeriya da ta yi wa Allah ta farfado da harkokin noma da sarrafa manja kamar yadda aka san ƙasar a baya. Kungiyar ɗalibai ta ƙasar ta yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya farfado da harkokin sarrafa manja da Allah ya wadata ƙasar da shi, ta yadda hajar zata wadata ƴan Najeriya da ma fitar da shi ƙasashen waje kamar yadda lamarin yake a baya. Kirin ƙungiyar ta NANS na zuwa ne bayan da Shugaban ƙungiyar masu samar da manja ta Najeriya Mista Alphonsus Inyang, ya ce Najeriya na kashe sama da daka miliyan 600 duk shekara wajen shigo da Manja daga katare duk da cewa Allah ya albarkaci ƙasar da kwakwan Manja.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba......
-
Kasuwar kayan abincin da ake samarwa a dakunan kimiyya na sake samun karbuwa
29/05/2024 Duración: 10minShirin na wannan mako ya duba yadda kayan abinci da ake samar wa a kimiyyance maimakon shuka ko yanka dabbobi ke kara budewa. Danna alamar saurare tare da Ahmad Abba
-
Hauhawar farashin kayayyaki na ci gaba da ta'azzara a Najeriya
22/05/2024 Duración: 10minShirin zai maida hankali ne kan hahoton baya-bayan nan da Hukumar Kididdiga ta Najeriya ta fitar wanda ya bayyana yadda kasar ke ci gaba da fuskantar karin hauhawar farashin kayayyaki musamman na abinci, mafi muni da kasar ta gani a sama da shekaru 20. Rahoton wanda National Bureau of Statistic ta fitar a makon da ya gabata, ya cewa an fuskacin hauhawan farashin kayayyaki da sama da kashi 33 da rabi cikin 100 a watan Afrilun da ya gabata.
-
CAC a Najeriya ta bai wa masu sana'ar POS wa'adin watanni biyu su yi ragista
15/05/2024 Duración: 11minShirin 'Kasuwa akai Miki Dole na wannan makon tare da Ahmad Abba ya maida hankali ne kan matakin gwamnatin Najeriya bukatar masu sana'ar POS da sauran masu mu'amala da na'urar da su garzawa hukumar rajistan kamfanoni ta kasar domin yin ragista kafin ranar 7 ga watan Yulin wannan shekara ta 2024.
-
Yadda wani kamfanin kasar Denmark ya shirya zuba jarin dala biliyan 6 a Najeriya
08/05/2024 Duración: 09minShirin kasuwa akai miki dole na wannan mako ya mayar da hankali kan shirin wani kamfanin Denmark na zuba jarin kudi dala biliyan 6 a fannin tashoshin jiragen ruwan jihar Lagas ta Najeriya Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba