Sinopsis
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Episodios
-
Dr Abubakar Sadiq Muhammad kan matsalolin tsaro a Najeriya
21/08/2025 Duración: 03minGwamnan Jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya, Uba Sani ya ce matakin soji kawai ba zai iya magance ayyukan ta'addancin da ake fuskanta a ƙasar ba. Gwamnan ya ce ya zama wajibi a magance matsalolin da ke haifar da matsalar baki ɗaya da suka haɗa da talauci da nuna banbanci da rashin shugabanci na gari da kuma bai wa matasa dama. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Abubakar Sadiq Muhammad, tsohon malami a jami'ar Ahmadu Bello akan matsalar ta tsaro a ƙasar. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu...................
-
Farfesa Balarabe Sani Garko kan rage farashin wanke ƙoda a wasu asibitocin Najeriya
20/08/2025 Duración: 03minShugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya amince da rage farashin wankin ƙoda daga naira 50,000 zuwa naira 12,000 a manyan asibitocin tarayya a faɗin ƙasar. Daniel Bwala, mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan Bayanan da suka shafi tsare-tsaren gwamnati ne ya bayyana hakan a shafin sada zumuntansa na X, inda ya ce matakin zai sauƙaƙa wa dubban marasa lafiya masu fama da ciwon ƙoda. An fara aiwatar da wannan mataki a manyan asibitoci kamar FMC Ebute-Metta da ke Lagos da FMC da ke Jabi a Abuja da UCH Ibadan da FMC Owerri da UMTH Maiduguri, yayin da za a ƙara wasu kafin ƙarshen shekara domin samun damar amfani da su a duk faɗin ƙasar. Sai dai da safiyar Laraba bayan rahotannin RFI, Gwamnatin Najeriya ta ɗan daidaita jerin sunayen manyan asibitocin ƙasar da za su ci gajiyar sabon tallafin domin sauƙaƙawa majinyta wanke ƙoda, inda aka ƙara asibitin koyerwa na Malam Aminu Kano da ke jihar Kano. Cikin sanarwar da ma'aikatar lafiyar ƙasar ta fitar, ta ce za'a ci gaba da ƙara wasu asibitocin ne dama sannu a hankali, amma
-
Farfesa Yusuf Abdu Misau akan rungumar abinicin da aka sauya wa halitta
19/08/2025 Duración: 03minGwamnatin Najeriya ta bayyana shirin amfani da malaman addini wajen wayar da kan jama'a wajen rungumar amfani da abincin da aka sauyawa kwayar halitta da ake kira GMO. Shugaban hukumar kula da irin wadannan abinci Farfesa AbdullahI Mustapha ya bayyana haka a tattaunawarsa da RFI Hausa. Ganin yadda jama'a ke dari darin amfani da irin wannan abinci, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin kula da harkar lafiya, Farfesa Yusuf Abdu Misau, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.
-
Tattaunawa da Janar Kukasheka mai ritaya kan kama shugabannin ƙungiyar Ansaru
18/08/2025 Duración: 03minGwamnatin Najeriya ta bayyana nasarar kama shugabannin ƙungiyar ƴan ta'adda da ake kira Ansaru mai alaƙa da Al'Qaeda, wadda tayi ƙaurin suna wajen kai munanan hare hare a jihohin Neja da kwara. Mai baiwa shugaban ƙasar Najeriya a kan harakokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya bada wannan sanarwar. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Tsofan kakakin runduna sojin Najeriya Janar Sani Usman Kukasheka ga kuma yadda zantawarsu ta gudana. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar hira......
-
Alhaji Mustapha Yusuf Mai Kalwa kan faɗuwar farashin kayan abinci a Najeriya
15/08/2025 Duración: 03minRahotanni daga sassan Najeriya na bayyana faɗuwar farashin kayan abinci, abinda zai taimakawa talakawa wajen samun sauki. Sai dai manoman ƙasar na ƙorafi a kan asarar da suka ce sun tafka. Domin tabbatar da samun saukin farashin, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shugaban ƴan kasuwar hatsi ta duniya da ke Dawanau a jihar Kano, Alhaji Mustapha Yusuf Mai Kalwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattawaunawar tasu.............
-
Abdulhakeem Funtuwa kan yunkurin dakatar da yaƙin Ukraine wajen mantawa da Gaza
14/08/2025 Duración: 03minA ranar Jumma'a ake saran shugaban Amurka Donald Trump zai yi wata ganawa da takwaransa na Rasha Vladimir Putin dangane da yadda za'a kawo ƙarshen yaƙin da ake gwabzawa a Ukraine. Sai dai wasu da bayyana damuwa kan yadda shugabannin suka manta da batun tsagaita wuta a yaƙin Gaza, ganin yadda ake ci gaba da asarar rayukan ɗimɓin rayuka. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr. Abdulhakeem Garba Funtuwa dangane da yunkurin ƙasashe duniyar na samaun tsagaita wuta da kuma watsi da halin da ake ciki a Gaza.
-
Ibrahim Wala kan bashin dala miliyan 300 da Najeriya ta ciwo daga Bankin Duniya
13/08/2025 Duración: 03minBankin Duniya ya ce ya amince da buƙatar bai wa Najeriya dala miliyan 300, domin amfani da shi wajen inganta rayuwar mutanen da rikici ya raba da muhallansu a yankin arewacin ƙasar. Sanarwar Bankin ta ce za ayi amfani da kuɗaɗen ne wajen tallafawa irin waɗannan mutane da waɗanda suka basu matsuguni domin ganin sun koma masu dogaro da kan su, maimakon dogara da kayan agaji. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Ibrahim Garba Wala, ɗaya daga cikin masu fafutukar kare hakkokin jama'a a Najeriya. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana................
-
Farfesa Bello Bada akan kisan ƴanbindiga 100 da sojin Najeriya suka yi
12/08/2025 Duración: 03minSojojin Najeriya sun yi nasarar hallaka ƴanbindiga sama da 100 a ƙaramar hukumar Bukkuyum dake jihar Zamfara, sakamakon wasu hare haren sama da suka kaddamar a kan su. Rahotanni sun ce sojojin sun yi amfani da bayanan asiri ne wajen kai harin kan ƴanta'addan waɗanda aka ce yawansu ya kai 400 a dajin a Makakkari. Wannan na daga cikin nasarorin da sojojin Najeriya suka samu a ƴan kwanakin nan. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna ad Farfesa Bello Bada na Jami'ar Usman Danfodio dake Sokoto, wanda ya ce wannan shi ne labarin da ƴan Najeriya ke farin cikin ji. Ga yadda tatatunawar su ta gudana a kai.
-
Hira da Aissami Tchiroma kan shirin gwamnatin Nijar na ƙarbe mahaƙun zinari
11/08/2025 Duración: 03minGwammatin Jamhuriya Nijar ta sanar da kwace kamfanonin hako zinari na ƙasashen ketare tare da mayer da su ƙarkashin kulawarta a cikin wani ƙudiri da shugaban mulkin sojin ƙasar Janar Abdurahmane Tiani ya sanya wa hannu a karshen mako. Haka ma gwamnatin ta hana fitar da ma’adinan ƙarkashin ƙasa zuwa waje ba tare da izini ba. Shiga alamar sauti domin sauraron karin bayani.......
-
Ladan Abdullahi Garkuwa kan shirin Ɗangote na rarraba mai da motocinsa sassan Najeriya
09/08/2025 Duración: 03minA Najeriya, ga dukkan alamu an samu rarrabuwar kawuna tsakanin dillalan man fetur, sakamakon shirin Aliko Dangote na jigilar man daga matatarsa da ke Lagos zuwa gidajen mai a sassan ƙasar. Yayin da shugabannin dillalan ke adawa da shirin Dangoten, kananan dillalan sun bayyana gamsuwar su da shirin, kamar yadda za kuji a tattaunawar Bashir Ibrahim Idris da Alhaji Ladan Abdullahi Garkuwa.
-
Jamilu Adamu kan manyan labaran jaridar Aminiya a wannan mako
08/08/2025 Duración: 03minKamar yadda aka saba a duk ranar Juma’a, muna kawo muku wasu daga cikin manyan labarun da Jaridar Aminiya da ke Najeriya ta ƙunsa. A wannan karon Nura Ado Suleiman ya tattauna ne da Jamilu Adamu, Editan shafin labarun ban Al’ajabi na wannan jarida.
-
Matsalolin tattalin arziki sun ka kawo ƙarshen matsayin matsakaitan mutane a Najeriya - Bincike
07/08/2025 Duración: 03minMatsalolin tattalin arziki a Najeriya ya taimaka wajen watsi da matsayin matsakaitan mutane da ke tsakanin al'umma, inda yanzu ake da attajirai ko matalauta kawai. Masanan na gabatar da dalilai daban daban da suka yi sanadiyar samun wannan matsala, wadda ta haifar da wagegen gibi a tsakanin al'umma. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar Bashir Ibrahim Idris da Dr Abbati Bako.......
-
Dakta Shu'aibu Shinkafi kan tsanantar hare-haren 'yan bindiga a Zamfara
06/08/2025 Duración: 03min'Yan asalin jihar Zamfara da ke Najeriya, na ci gaba da bayyana matuƙar damuwarsu dangane da ƙaruwar hare-hare da kisan jama'a da 'yan bindiga ke yi. Mazauna wannan jiha da ke Arewa maso Yammacin ƙasar, sun buƙaci haɗin kai tsakanin gwamnatin jihar da ta Tarayya da zumar samar musu mafita ta dindindin. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dakta Sulaiman Shu'aibu Shinkafi daga jihar. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
-
Dakta Auwal Aliyu kan zanga-zangar tsaffin sojojin Najeriya
05/08/2025 Duración: 03minWani adadi da dama na tsaffin sojojin Najeriya da suka ajiye aiki bisa raɗin kansu, sun mamaye gaban ginin Ma’aikatar Kudin ƙasar, inda suka gudanar da zanga-zanga kan rashin biyansu wani kason kuɗaɗensu na Fansho. Zanga-zangar ta safiyar jiya Litinin, na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan makamanciyarta da tsaffin jami’an ‘Yansanda suka yi kan haƙƙoƙinsu. Domin gano bakin zaren warware matsalar tsaffin jami’an tsaron Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Auwal Aliyu Abdullahi, mai magana da yawun Kwamitin musamman da ke kula da walwalar tsaffin sojoji a Najeriya. Shiga alamar sauti domin sauraron ckakkiyar tattaunawar.
-
Dakta Isa Sanusu kan kin hukunta ƴansanda da suka murƙushe zanga-zangar yunwa
04/08/2025 Duración: 03minƘungiyar kare hakkin bil’adama ta Human rights watch ta koka kan yadda har yanzu gwamnatin Najeriya ta gaza ɗaukar mataki kan ƴan sandan da aka zarga da kisan mutane lokacin zanga-zangar yunwa da ta faru a ƙasar a bara. Baya ga haka kuma ƙungiyar ta ce lokaci yayi da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yiwa iyalan ɗan gwagwarmayar nan Abubakar Dadiyata bayanin halin da yake ciki shekaru 6 bayan ɓatansa Shiga alamar sauti don sauraron cikakken bayani....
-
Tattaunawa da Barista Abdullahi Jalo kan taron jagororin Arewacin Najeriya
31/07/2025 Duración: 03minJagororin yankin Arewacin Najeriya sun kammala taron yini biyu da duka gudanar a Kaduna, don bibiyar alkawurran da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya ɗaukar wa yankin a lokacin yaƙin neman zabe. Wannan dai na zuwa ne bayan da wasu suka yi zargin cewa an maida yankin saniyar ware duk kuwa da irin gudunmuwar da ya bayar a lokacin zaɓen baya. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar Khamis Saleh da Barista Abdullahi Jalo...........
-
A Najeriya duk da zambaɗawa wutar lantarki kuɗi har yanzu ba ta sauya zani ba
30/07/2025 Duración: 01minA Najeriya, duk yadda mahukunta ke tsawwala kudin wutar lantarki, tare da bijirowa da dokokin da suke ganin za su inganta bangaren samar da wutar, har yanzu dai da sauran rina a kaba a game da ƙarancin wutar. Akan haka ne Michael Kuduson ya tattauna da ɗan gwagwarmaya a jihar Kanon Najeriya, Kwamared Belllo Basi, ga kuma tattaunawarsu.
-
Hira da Sani Roufa'i kan cika shekaru biyu da yin juyin mulki a jamhuriya Nijar
28/07/2025 Duración: 03minRanar 26 ga watan yuli ne aka cika shekaru biyu da kifar da gwamnatin Bazoum Mohamed a Nijar, albarkacin wannan rana shugaban ƙasar Abdurahmane Tchiani ya gabatar da jawabi inda ya bayyana halin da kasar ke ciki. Ra'ayoyi jama'a dai sun sha bamban a kan tafiyar ƙasar a yanzu. Shiga alamar sauti domin jin cikakkiyar hira da Ibrahim Tchillo ya yi da Sani Roufa'i masanin halayya zamantakewa a jamhuriya Nijar....
-
Dr Abdulƙadir Suleiman kan dalilan da ya sanya duniya ta mance da yaƙin Sudan
25/07/2025 Duración: 03minSama da shekaru biyu bayan ɓarkewar yakin basasar ƙasar Sudan, kasashen duniya sun kau da kan su, yayin da ake ci gaba da hallaka fararen hula. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Abdulkadir Suleiman Muhammad, a kan dalilin da ya haifar da yaƙin da kuma yadda ƙasashen duniya suka juyawa ƙasar baya. Latsa alamar sauti domin sauraren hirar...
-
Farfesa Abba Gambo kan barazanar yunwa da mutane sama da miliyan 3 ke fuskanta
23/07/2025 Duración: 03minƘungiyar agaji ta ICRC ta bayyana cewar akwai yiwuwar fuskantar matsalar yunwa a arewa maso gabashin Najeriya sakamakon tashin hankalin da ya tilastawa manoma ƙauracewa gonakin su. Latsa alamar sauti domin sauraren tattaunawar Bashir Ibrahim Idris da Farfesa Abba Gambo...