Sinopsis
Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Alumma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalinariziki, aladu da dai sauransu
Episodios
-
Kan yadda duniya ta yi bankwana da shekarar 2024
31/12/2024 Duración: 10minA yayin da ake bankwana da shekarar 2024 shuwagabanni daga kasashen Duniya na fuskantar tarin kalubale da suka hada da rikice-rikice,yake-yake harma da wasu matsalolin da suka shafi sauyin yanayi da matsin tattalin Arziki da sauran su. Wasu abubuwa ne baza ku iya mantawa ba kuke tsoron dakon su zuwa sabuwar shekara?Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin, tare da Hauwa Garba Aliyu Zaria.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa mabanbanta
27/12/2024 Duración: 09minA yau juma'a kamar yadda aka saba kuna aiko mana da saƙonnin ra'ayoyinku kan abubuwan da ke ci muku tuwo a ƙwarya a fannoni daban-daban na rayuwa, kama daga fannin tattalin arziki, tsaro, lafiya, siyasa da sauransu. Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyi mabanbanta...
-
Ra'ayoyin masu saurare: harin soji kan Lakurawa ya hallaka mutane fiye da 10
26/12/2024 Duración: 09minAna fargabar al'umma da dama sun mutu wasu kuma sun jikkata sakamakon wani hari da jirgin yaƙi na soji ya kai kan Lakurawa a wasu ƙauyuka da ke Sokoton Najeriya. Ana kallon wannan harin a matsayin na kuskure kuma ba wannan ne karon farko da hakan ke faruwa ba a arewaci da wasu Najeriya.Latsa alamar sauti domin sauraren mababanta ra'ayoyi a cikin shirin da Abida Shu'aibu Baraza ta jagoranta...
-
Ra'ayoyin masu saurare kan rasa rayuka da aka yi yayin turmutsitsi a Najeriya
23/12/2024 Duración: 10minAƙalla mutane 60 suka rasa rayukansu a sassan Najeriya, yayin turmutsitsin karɓar tallafin abinci da kuma taron bikin ƙarshen shekara na yara a jihohin Anambra, da Oyo da kuma birnin Abuja. A yayin da ‘yan Najeriyar ke tofa albarkacinsu kan lamarin wasu na ɗora laifin aukuwar haɗurran akan gazawar mahukunta wajen samar da tsarin bai wa mutane kariya yayin taruka, yayin da wasu ke ganin ɗaiɗaikun masu raba tallafin ke da alhaki la’akari da cewar suna yin hakan ne ba tare da tsari ko sanin hukuma ba.Wannna shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai.Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin...
-
Ra'ayoyin masu saurare kan kasafin kuɗin 2025 da shugaban Najeriya ya gabatar
19/12/2024 Duración: 11minA ranar Laraba ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gabatar da kasafin kudin ƙasar na shekarar 2025 na naira Tiriliyan 47.9. Sai dai wani batu da ya haifar da muhawara a tsakanin ‘yan Najeriya dangane da kasafin kuɗin na baɗi, shi ne yadda aƙalla kaso 30 zuwa 32 na yawan kuɗaɗen za su tafi a biyan basuka ko kuma kudin ruwan basukan, kwatankwacin naira tiriliyan 15 da biliyan 800, adadin da ya zarce yawan kudaden da aka warewa tsaro, ilimi, lafiya da manyan ayyuka.Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a yau.Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin tare da Kabiru Mohammed Dan Bauchi...
-
Ra'ayoyin masu sauraren Rfi biyo bayan lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Afrika na 2024 daga Lookman
17/12/2024 Duración: 10minA bikin da aka gudanar a birnin Marrakech na Morocco, Lookman ya shiga gaban ƴan wasan irinsu Simon Adingra na Ivory Coast da Achraf Hakimi na Morocco da Serhou Guirassy na Guinea sai kuma mai tsaron gidan Afrika ta Kudu Ronwen Williams.Tauraruwar Lookman wanda ke wasa a ƙungiyar Atalanta na haskawa a bana, musamman idan aka yi la’akari da bajintar da ya nuna wajen zamowa ɗan wasa na farko tun daga shekarar 1975 da ya zura kwallaye uku a raga cikin mintina 26.Masu saurare sun bayyana fatan da suke da shi a cikin wannan shiri..........
-
Ra'ayoyin masu saurare kan shirin maja tsakanin Atiku da Obi a zaɓen 2027
12/12/2024 Duración: 10minTsohon mataimakain shugaban Najeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a zaben 2023 da ya gabata Atiku Abubakar da kuma ɗan takarar LP a 2023 Peter Obi na shirin haɗewa domin kawar da gwamnatin APC wadda a cewarsu ta gaza, lamarin da ke zuwa tun kafin kakar zaɓen na shekarar 2027. Sai dai a martaninta, jam’iyyar APC ta ce babu wata haɗaka da za ta iya taka wa shugaba mai ci birki.Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai.Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin...
-
Ra'ayoyin masu saurare kan haramcin fitar da masara daga Najeriya
11/12/2024 Duración: 10minKamar yadda aka saba, RFI Hausa na bai wa masu saurare damar bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwa da dama da ke ci musu tuwo a ƙwarya. Majalisar dattawar Najeriya ta amince da wani kuɗirin doka da ya haramta fitar da duk wata masara mai yawa da ba'a sarrafa ta ba daga ƙasar zuwa ƙasashen waje, kuma ta tanadi hukuncin ɗaurin shekara guda ga duk wanda ya yi kunnen ƙashi.Wannan shi ne maudu’in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a yau.Latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyin mabanbanta..
-
Ra'ayoyin masu saurare kan kifar da gwamnatin Al-Assad na Syria
10/12/2024 Duración: 09minA ƙarshen makon da ya gabata ne ƴan tawaye suka kifar da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad na Syria da zuri’arsa suka shafe shekaru 50 su na mulki a ƙasar. Rahotanni dai na cewa Al-Assad da iyalansa sun tsere daga ƙasar inda ake kyautata zaton cewa Rasha ta basu mafaka, lamarin da ƙasar Rashan ta musanta, yayin da ƙasashen duniya ke tofa albarkacin bakinsu.Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin tare da Hauwa Aliyu..
-
Ra'ayoyin Masu Saurare kan zaɓen Ghana
09/12/2024 Duración: 09minMataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar jam’iyya mai mulki a Ghana, Mahamudu Bawumia ya amince da shan kaye a zaɓen ƙasar, inda ya taya tsohon shugaban ƙasa John Mahama murnar lashe zaɓen. Wannan ya biyo bayan zaɓen shugaban ƙasar da aka yi a Asabar ɗin ƙarshen mako 7 ga watan Disamba, wanda rahotanni suka tabbatar da cewa ya gudana cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.Shin ya ku ka kalli yadda zaɓen na Ghana ya gudana?Me za ku ce kan yadda Bawumia ya amince da shan kaye tun kafin a fitar da sakamakon zaɓen?Wane darasi ku ke ganin ƴan siyasa a yankunanku za su koya daga zaɓen Ghana?Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin
-
Ra'ayoyin masu saurare kan caccakar tsarin zaɓen Kamaru
06/12/2024 Duración: 09minA Jamhuriyar Kamaru, wani babban limamin cocin Katolika a Duwala, Archbishop Samuel Kleda ya caccaki tsarin zaben ƙasar, wanda ya ce an tsara shi ne don bai wa shugaba mai ci damar ci gaba da yin kane-kane kan madafun iko, yana mai cewa akwai buƙatar gyara in dai dimokaradiyyar ake so. Latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi...
-
Ra'ayoyin masu sauraro kan kame mafi girma da EFCC ta yi a Najeriya
04/12/2024 Duración: 09minA Najeriya, kwanan nan ne kotu ta karbe wani rukuni mai ƙunshe da gidaje 753 mallakin wani tsohon gwamnan babban bankin ƙasar, nasara mafi girma da hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati ta taɓa samu a cikin sama da shekaru 21 da kafuwarta. Wannan shi ne maudu’in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a yau. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin tare da Oumaru Sani:
-
Ra'ayoyin masu sauraro kan ranar masu buƙata ta musamman ta duniya
04/12/2024 Duración: 10minKamar yadda aka saba, RFI Hausa na bai wa masu saurare damar bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwa da dama da ke ci musu tuwo a kwarya. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware ranar 3 ga watan Disambar kowacce shekara a matsayin ranar masu buƙata ta musamman, wato mutane da ke rayuwa da wata naƙasa a fadin duniya.Wannan shi ne maudu’in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a yau.Ku latsa alamar sauti domin sauraren shirin tare da Hauwa Halliru Gwangwazo:
-
Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa da dama
29/11/2024 Duración: 10minKamar yadda aka saba, RFI Hausa na bai wa masu saurare damar bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwa da dama da ke ci musu tuwo a kwarya. Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a
-
Kan ficewar Nijar, Mali, Burkina Faso daga ECOWAS
21/11/2024 Duración: 10minA watan Janairun shekarar da ta gabata Jamhuriyar Nijar da wasu ƙasashen Sahel 3 su ka bayyana aniyar ficewa daga ƙungiyar ECOWAS ta ƙasashen yammacin nahiyar Afrika a hukumance. A halin da ake ciki, watanni 3 ne kacal su ka rage wa’adin ficewar su ta cika, bayan sanar da ECOWAS batun janyewar kamar yadda dokokinta su ka tanada.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
-
Kan yadda 'yan bindiga suka kone amfanin gonar da aka girbe a arewacin Najeriya
14/11/2024 Duración: 10minA Najeriya a yayin da aka fara girbin amfanin gona, rahotanni daga sassan ƙasar sun bayyana yadda hukumomi, kamfanoni da ɗaiɗaikun mutane ke sayen ɗimbim hatsi su na tarawa, lamarin da ya haddasa tsadar su jim kaɗan bayan da farashi ya fara saukowa. A cewar masu lura da al’amura, wannan lamari zai ta’azzara tsadar kyayyakin abinci, ganin ayyukan ƴan bindiga su ka hana al’ummomi da dama yin noma.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
-
Kan yadda kamfanoni ke saye amfanin gonar da aka girbe a Najeriya
13/11/2024 Duración: 09minA Najeriya a yayin da aka fara girbin amfanin gona, rahotanni daga sassan ƙasar sun bayyana yadda hukumomi, kamfanoni da ɗaiɗaikun mutane ke sayen ɗimbim hatsi su na tarawa, lamarin da ya haddasa tsadar su jim kaɗan bayan da farashi ya fara saukowa. A cewar masu lura da al’amura, wannan lamari zai ta’azzara tsadar kyayyakin abinci, ganin ayyukan ƴan bindiga su ka hana al’ummomi da dama yin noma.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
-
Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa da dama
08/11/2024 Duración: 10minKamar yadda aka saba, RFI Hausa na bai wa masu saurare damar bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwa da dama da ke ci musu tuwo a kwarya. Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a
-
Ko meke haifar da tarnaƙi a tabbatar da tsaro a arewacin Najeriya?
22/10/2024 Duración: 04minRa'ayoyin masu saurare na wannan rana ya mayar da hankali kan yadda aka kwashe watanni biyu bayan da shugaban kasa ya umarci hafsoshin tsaro da su tare a jihar Sokoto don tabbatar da tsaro, amma har yanzu 'yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare ba kakkautawa. Shin ko me ke haifar da tarnaki ga kokarin tabbatar da tsaro a arewacin Najeriya?Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna
-
Ra'ayoyin masu saurare kan batutuwa da dama
18/10/2024 Duración: 10minKamar yadda aka saba, RFI Hausa na bai wa masu saurare damar bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwa da dama da ke ci musu tuwo a kwarya. Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a